
Wadansu 'yan bindiga sun kashe 'yan sanda "bakwai" a
Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Talata.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan birnin DSP
Anjuguri Manzah ya tabbatar da faruwar al'amarin a wata
sanarwa daya aike wa hb.
Sai dai bai yi karin haske ba game da adadin jami'ansu da
suka rasa ransu sanadiyyar abin da ya kira "bata-kashi",
amma ya ce an fara gudanar da bincike don gano maharan.
Rahotanni sun ce al'amarin ya faru ne a mahadar unguwar
Galadimawa da ke kan hanyar filin jirgin saman Abuja.
'Yan bindigar sun harbe 'yan sanda ne lokacin da suke wani
shingen bincike, inda 'yan bindigar suka rika yin harbi daga
cikin wata mota da suke tukawa, a cewar rahotanni.. Ibrahim m ali. daga zamfara
Thank's for reading my article
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 'bakwai' a AbujaCreated at 2018-07-03 15:43:21

0
Rate up
Star