
Yau kwanaki hudu sojojin saman Nigeria suke
ruwan wuta a kan tawagar 'yan ta'addan da sukayi
hari a sansanin sojoji dake kauyen Metele karamar
hukumar Guzamala jihar Borno
Jiragen yakin sojojin saman Nigeria kirar Mi-34M
wani samfurin jirgin yaki ne wanda harsashin
bindiga baya hudashi sunyi ruwan wuta daga sama
da manyan bama-bamai masu linzami akan 'yan
ta'addan, dukkan kayan yakin da suka dauka a
sansanin sojoji dake Metele jiragen yakin sun
lalata, kuma zuwa yanzu babu wanda ya tsira daga
cikin 'yan ta'addan da sukayi harin
Bayan 'yan ta'addan sunyi harin Metele suka kashe
mana sojoji tare da kwashe kayan yakinsu, sai
suka nufi kauyukan Tumbun-Rego da Kangarwa da
Mainok a daidai lokacin da jiragen leken asiri ta
sararin samaniya suka bi diddiginsu, kafin nan sai
aka aiko da jiragen yaki dauke da bama-bamai da
manyan bindigogi masu cin nisan dogon zango
akayi kaca-kaca da tawagar 'yan ta'addan, wanda
ya tabbata cewa babu wanda ya tsira daga cikinsu
Hatta 'yan ta'addan da sukayi kokarin tsallaka
bodar Nigeria da makaman da suka samu a harin
Metele jiragen yakin Nigeria yabi ta kansu an
shefesu basu samu hanyar tsira ba.
Bayanan sirri ya tabbatar da cewa kwamandojin
'yan ta'addan da sukayi hari a Metele ba 'yan
Nigeria bane, akwai 'yan Algeria, Mali da Chadi,
cibiyar ISWAP wanda ISIS da kanta ta dauki nauyin
harin.
Sojojin da suka tsira a harin Metele sunce sunji
'yan ta'addan suna magana da harcen Larabci da
Faransanci, sun saka kayan sojoji irin wanda
rundinar sojin hadin gwiwa na kasashe Multi
National joint Task Force (MNJTF) tsakanin
tsakanin Nigeria, Kamaru, Nijer da Chadi suke
sakawa, da suka iso sansanin sojojin Metele su a
tsammanin sojojin dake gurin sun dauka cewa 'yan
uwansu sojoji ne suka kawo musu ziyara, kawai
sai suka bude musu wuta
Alhamdulillah su ma 'yan ta'addan basu tsira ba,
Kuma yau kwana hudu kenan shugaba Buhari yana
ta ganawa da manyan shugabannin tsaron
Kasarmu Nigeria don ganin abinda ya faru a Metele
bai sake faruwa ba
Ina wadanda sukayi murna da abinda aka yiwa
sojojinmu a Metele??? Insha Allahu murnanku zata
koma bakin ciki!!!
Allah Ka karawa sojojinmu taimako da nasara akan
'yan ta'adda manyansu da kananansu Amin
Thank's for reading my article
LABARI MAI DADICreated at 2018-11-27 10:23:25

0
Rate up
Star