WELCOME TO HAUSABOY


This site
Ameena Part 1 - XtGem.com
Old school Swatch Watches

Ameena Part 1

Ameena Part 1
BY: IBRAHEEM M ALI IBBI . Zaune take cikin ofis dinta ta zabga uban tagumi banda hawaye babu abinda ke shatata afuskarta kallo daya zakaimata kasan tana cikin tashin hankali. Abokin aikintane Dr.hafiz yashigo da sallama turus yayi dayaga halinda take ciki. Jikinshi yai sanyi sosai yasamu ya zauna kamin ya saita nutsuwarshi. Aiman aiman dan Allah kiyi shiru kidaina wannan kukan tunda banga amfaninshiba kukannanfa ba magani zaiyi mikiba tomezaisa kita kuka. Cikin wata salahar murya tace Dr.dole inyi kuka wlh ina mamakin abinda dadyna ke niyyar yimin saikace wadda bata da gata koda yake dama haka nataso banida wani gata saina Allah amma nayi tunanin yanzu zasubarni hakanan dan hankalina ya kwanta saigashi sunkuma kawa wani mummunan tashin hankali cikin rayuwata. Pls Dr.Aiman kiyi hakuri Dan Allah domin kisami nutsuwa nisainaga kawai ki kyale komai kikai kukanki wajan Allah ki yadda da qaddara saikiga kinsami nutsuwa ko kalli yadda duk kika koma kinrame sosai wlh. Shikenan nagode Dr.Allah yasaka da alkhairi. Yauwa kokefa sarauniyar mata. Saida ya rakani har wajan motata sannan mukai sallama. Rashe rashe nayi agadona ina maida numfashi.tabe baki tayi kamin tace matar mahaukaci ya aikin.wani murmushin takaici nayi sannan nace alhamdulillah ina godema Allah daya hadani da mahauci batare danabi boka ko malamba aikinga dole ingodema allah. Wani mugun tsaki taja sannan tabarmin dakin ahankali nafara kuka ina neman daukin ubangijina domin nasan bemanta daniba. Hello dady zani wajan mama idan kabari ba dadewa zanyiba zandan dubatane batajin dadi. Ok amma karki jima kice ina gaisheta sosai. Saida nai sallar isha,i sannan nashirya cikin doguwar riga ta atamfa sannan nadora hijab nai waje matar dadyna na zaune falo tana taunar cingam kamar karuwa koda yake meye marabar dambe da fada. Ga aunty ga aunty cewar kannena da muka hada uwa daya dasu rungumarsu naitayi inajin dadi sannan nabasu tsarabarsu nasamu sukabarni da mama kallona take cike da tuhuma niko sai zare manyan idanuna nake kamar antsare makaryaci. . Aiman kinada hankali kuwa kinkoga yanda kika koma.duk kinfige kin lallace wato bazaki yadda da gaddarabako komifa dayasameki da sanin Allah jarabawace kisamu ki cinyeta kinji aiman kiyi hakuri Dan Allah ki kwantar da hankalinki. Cikin kuka na rungume mahaifiyata mama kitayani da addua kullun bansamun barci hankalina yagaza kwanciya mama anya kuwa dady shiya haifeni kodai nidin diyar wanice ba dadyba. Karki kuma cewa haka domin mahaifinki fin karfinshi akai kuma badan komai akai hakanba saidan hankalina yatashi.amma wlh nasan dadynki bazaimiki hakaba. Mama ki kalli tsntsar kyawu da Allah yabani kamar ninayi kaina babu abinda narasa ajikina Allah yaimin daukaka nazama babbar likita dukda karacin shekaruna Allah yaimin farin jini kowa nasan yasame amma arasa wanda za ahadani dashi sai mahaukaci mahaukacimma wanda masifar shaye shaye sabama Allah ya haukatar. Dakin yai shiru sai sheshshekar kukana datacika dakin. Ki kwantar da hankalinki ke diya macece zaki iya daukar kowane hali nada namiji harki saitashi kan yanda kikeso domin awajanki zai koyi wasu abubuwa sabida haka ki tsaya tsayin daka wajan ganin kinshawo kan matsalar gidanki sannan kuma karki bari kowa yasan sirrin gidanki domin anyine domin aga yanda zamuyi to aishi Allah ba azzalumin bawanshi bane Allah yasa hakan shine kwanciyar hankalinmu. Mama maganar aikina kuma. Kibarta aiman kiyi hakuri Allah ya zabamiki mafi alkhairi cikin rayuwarki. Wayata na ciro dataketa ring nace mama kingani mahaifiyarshece ke kirana. Bayan mungaisane take cewa bazan gaji da baki hakuriba domin antauyeki da yawa amma dan Allah kiyi hakuri ki rungumi qaddara kinji diyata inasonki inasan zama dake kuma naimiki alkawarin matukar Allah yabawa ammar lfy kikaji bakisonshi har lokacin to zansa ya rabu dake domin kisami nutsuwa kinji Allah yaimiki albarka yashigo dake cikin family dina da SA a Ajiyar zuciya na sauke mama taimin zuru tana kallona.domin taji kai.shikenan Allah yasa mudace cewar mama. . Biki akeyi nafada da bada lbr domin mahaifina hamshakin me kudine haka kuma iyayen angon nawa. Duk wani wanda ya halarci bikin yasan naira ta koka. Wani abin mamaki shine babu amarya babu ango wajan wannan shagalin biki. Kwance nake inata makyarkyata kan gadona kanwar mamata tashigo alamun tashin hankali ya bayyana afuskarta ta zauna gefen gadon tare da yaye bargon dana rufa dashi sannu Aiman kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki insha Allah saikinyi alfahari da wannan auran domin anyishine domin ki wulakanta amma insha Allah saidai wanda ya shiryashi ya wulakanta domin babu wanda kika cuta haka babu me cutarki kidaina kuka kinji. Tashi muje asbt kamin yan daukarki suzo dan Allah kibar kukannan wlh yana tashin hankalina sosai ki kwantar da hankalinki kiba marada kunya kinji Allah yaimiki albarka. Kwalliya taimin me kyawun gaske nafito abalarabiyata sak kamar mutun ya saceni dan kyau ammafa damuwa fal cikin raina domin fuskatama ta bayyana hakan. Asbt danake aiki ta kaini magunguna Dr hafiz yahadamin sannan mukai sallama Bayan sallar isha,i akazo daukata kukam nashashi kamar wadda tarasa iyaye. . . Tunsuna lallashina har sukagaji suka kyaleni ammafa duk wanda ke cikin motar yana cikin damuwa domin duk yan uwan mamatane wa inda sukasan ciwona da damuwata. Munsami tara mekyau da girmamawa daga dangin mijin nawa. Hakanyasa nadan sami saukin zafin da zuciyata keyi. Qaton gidane sosai wanda aka kawatashi da kayan alatu narayuwa. Bangaren hajiyarshi aka barni harsaida kowa ya watse daga dangina. Sannan takawomin abinci. Da lemo ammakasa cinai. Taita mita amma nace mata nakoshi. Wasu mata nagani wanda na tabbata kannenshine su biyu halimatu da sadiya yan biyune ko wacce da goyanta. Suketa nannan dani kamar zasu goyani komi sunce aunty yayinda nikuma kunya tahanani sakewa ga mugun zullumin dayake damun zuciyata na haduwa da mijina shin haukan nashi na dukane ko jifa ko cizo lallai ina tare da wahala. . Sai wajan 11 nadare umman tace muje narakaki bangarenki kinji. Zuciyata kamar zatayo waje sabida zullumin yanda zanganshi wayyoni. Gaskiya tsarin da akaimin yaimin kyau sosai domin dady yakashe nera haka mama. Ko zama banyiba tace wancan saman na mijinkine zo muje ki Ganshi Dan Allah kiyi hakuri kuyi zamanku lfy har Allah yakawo ranar dazaisami waraka domin har yanzu inaji ajikina zai warke shiyasa nakasa fidda raina ga hakan. Tana rike da hannuna muka shiga dakin wayyo Allah saura kadan na sike sabida zarnin fitsari.yana kwance dagashi sai gajeran wando kafafunshi nasama yayinda uwarjikin ke kasa. Ammar ammar ga sabuwar aunty nakawo maka tashi ka ganta kaji. Innalillahi wa inna ilaihirraji,un zuwayai ya duka gabana aunty ina kwana umma taki amsamin. Wasu hawaye suka zubomin wanda na tabbata na tausayinshine. Umma meyasameshi haka naga kamar rayuwar yara yakeyi. Kwarai kuwa aiman domin har fitsarin kwance yakeyi hancinki be jiyemikiba wlh babu asbt dabamu kaishiba nadaga kasashen duniya amma babu wani cigaba da akasamu hakanyasa muka zubama sarautar Allah ido. Kije ki huta zanbaki labarin waye ammar domin kisami nutsuwar zama dashi karkije dashi dakinki domin yanada bannar masifa. Ina komawa dakina nai wanka nai nafilata kamar yadda nasaba nai addua sosai kan wannan jarabawa da Allah yadoramin inafatan yabani ikon cinyeta duka. Harna kwanta amma na mike tausayi yabani yanzunan haka zai kwana cikin wannan mugun zarni. Kai ina mijinane dole nakula dashi domin nasan sai Allah ya tambayemu irin zaman da mukai da mazajenmu bawai dan besaniba no saidan kafama kanka shaida. Cikin sanda na nufi dakinshi azuxiyata ina tsinema wanda yaimai sherin hauka domin cemin akai shaye shaye ya haukatar dashi. Ina bude dakin naga yaiwani lama lama barci kawai yake.nadan bubbugashi cikin muryar kuka yaiwasu surutai yaci gaba da barcinshi. Dakyar nasamu yatashi zaune hadda kukanshi bawan Allah nace zo muje dakina mu kwana kaganan zarni yakeko nafada ina dode hancina. . Lallabashi nayi yabini sannan narufe dakin ina rike da hannunshi har dakina kai tsaye wajan mirror dina ya nufa nace inka taba zamu bata zokai wanka kaji. Hankalinshi nakan kayan kwalliyar da suka cika mirror din yace aiban iyaba nan kawai nake wankewa yanunamin fuskarshi da kafafu.kirjina yaiwani dumm auko idan . be wankaba bazan iya kwanciya dashiba. Taho inhada maka ruwan sai innuna maka yanda zakayi. Kamin nahado ruwan harya tube wandon jikinshi. Aunty inasan wankan yimin da kanki kutt nakusa suma danaganshi azahirinshi tsaye yana sosa sumar kanshi. Dakyar nasamu na daidaita nutsuwata na cire tsoro da fargaba da kunya nafara wanke jikinshi tass har kuka yake wai zafi wankan. Wajan shafane naita fama dashi bayan nagama yimishi shafar saiya samin kuka waisainaimai kwalliya hakanan nasamu nashafa miki hoda nakama mishi hannu muje kai fitsari ka kwanta inkaji wanima katasheni in rakaka kaji Ko barcin kirki banyiba sabida zullumin zaimin fitsarin kwance. Sanda akafara kiran sallah asbah yatasheni wai fitsari zaiyi. Dasauri narakashi yayo namatsamai mukai sallah tare sannan muka koma sai lokacin nasami barci. . Wajan 9 naji muryar me aikin umma tana sallama namike ahankali tare da amsawa. Na gaisheta ta amsa da hanzari hadda dan russunawa domin batazaci hakaba ganin irin kyawun danake dashi gakuma dukiya wanda yawancin mata zakasamesu da wannan mugun girman kan natsiya. Dama hajiyace tace nakawo muku abinci gayacan nashirya afalonki. Shikenan nagode sai anjima zanshigo mu gaisa. Ina komawa naganshi zaune bakin gadon yanata hamma bako rufe baki. Kai ammar kadingasa hannunka kana rufe bakinka kadda bera yashige maka ko. Saida nasashi ya wanke bakinshi sannan mukai falo cin abinci saura kadan nazubar da hawaye domin yanda yakecin abincin yanayi yana wasa kamardai yaron da baiwuce shekara huduba. . Yai wani kaca kaca da wurin saida nabari yagama sannan nabashi kayan yamaida kichin nikuma na gyara wajan. Wani uban zillo yayi yafado kaina tare dasa kuka.afirgice nace meyene me akaimaka bayanshi ya nunamin wai na sosa mishi Haushi yakamani ohni naga takaina amarya kenan harna fara aikin megida. Janshi nayi naimai wanka sosai na gyara sumar kanshi na aske sajen dayaimai yawa na shafeshi da mai hadda hoda sannan nace kazaunanan in dauko maka kaya kaji be kalleniba ya amsa domin jelar gashina ta daukemai hankali da ita yake wasa. Karamar riga da wandon jeans na daukomishi kai haushi waiko wando be iya sawaba. Harna fito wanka yanata fama yakasa sawa. Saida nagama kwalliyata sannan nasamishi wayyo gayu inama ammar lafiyarshi qalau wlh danayi dacen mijin aure nanuma taro. Shikanshi sai kallon kanshi yakeyi a mirror yana murmushi. Muje mugaido umma saimudawo muyi aikin gidako. Washemin fararan hakoranshi yayi batare dayayi maganaba. Tsabar mamaki yasata kasa tashi ammafa bakinta har kunne sabida murna. Kasa naduka nagaidata sannan shima ya gaidata. Umma kingani aunty taimin wanka da kwalliya nayi kyau ko.kunya takamani itako sai murmushi take.Aiman meyasa baki bari kin hutaba daga zuwa saiki fara wahala. Haba umma babu wata wahala wlh. Allah yaimuku albarka yabawa mijinki lfy. Munjima zaune nace bari mukoma can akwai dan gyare gyaren dazanyi. Kibari uwani tayi miki gatanan zuwa. A a umma tabarshi kawai.inamikewa shima yamike har yana kokarin kifawa kasa yabiyoni. Komawa nayi daki nasauya kayan jikina nanafi dakinshi nai mamakin aikin dayayi koda yakezuciyarce ta yara ba jikinba Saida naga dakin yaimin yanda nakeso sannan hankalina ya kwanta tsalle yaiyafada saman gadonshi yanacewa inye ansamin sabo dakina yanayin kanshi. . Murmushi nabishi dashi yayinda idanuna suka kawo kwallah tausayinshi yakamani kai duniya dole mutun yaji tsoran Allah kuduba lafiyayyan mutun me tarin kyawu da kwarjini ga ilmi da tarin dukiya amma lokaci daya Allah ya maida zuciyarshi ta yara wadda babu komai ciki saitarin wauta da kuriciya. Munayin sallar azhar muka kwanta barci domin nai aiki da yawa jikina yagaji sosai. Dakanshi yatasheni sallar la asar naji dadi sosai yanzuma saida naimai wanka na nunamishi yanda zaisa kaya sannan nasamu nashiga nayo wankan. Muje wajan umma hira yanzu auntyna kinyi kyau sosai gashinki har baya nima inasan nawa yayi irin naki. Ammar kadaina cemin aunty ni kanwarkace kuma matarka kai mijinane niyakamata na girmamaka bakaiba kaji sunana Aiman haka zakadinga kirana kaji. Murmushi yayi kawai bana tunanin yagane wannan dogon bayanin danaimishi kai gaskiya inajin tausayin mijina sosai kuma inamishi fatan samun sauki. Kwance nake nayi filo da cinyarshi.yayinda shikuma yaketa faman yamutsar gashin kaina wai ala dole saiyayimin kitso. Umma tai sallama itada wani matashi abayanta nai saurin tashi zaune kunya ta isheni. Ammar ya kara shigewa jikina tare da saka kanshi akirjina yai lamo wayyo kunya jinai kamar intsaga kasa inshige. Ammar ga ummafa tazo kaishiru. Kaga hadda bakoma tazo.banza yaimin.umma tace rabudashi yau miskilanci nakusa. Aiman ga babban abokin mijinkinan kuma amini dan uwa. Gafda bikinku yatafi london sai jiya yadawo dacan shike kulada ammardin duk da cewa kullun saisunyi fada. Har russunawa nayi sannan nagaidashi ya amsa cikin farin ciki da walwala yadora dayimin nasiha kan muhimmancin aure da irin ladar da zansamu adalilin rungumar qaddara danayi na zaunada wanda bashida lfy bayan ina cikin kuruciyata da kwarjinina. Nan danan mukaita hira har yamma sannan sukaimin sallama. Mukuma muka koma dakinmu domin gabatar magriba ina mamakin sabon da mukayi da ammar domin yanzu ko kwanciya zanyi saiya rungumeni tsamtsam ajikinshi.dukda cewa yanadamuna da surutan shirme amma bana damuwa sam. Satina uku najema ummanshi da maganar aikina.tace babu matsala nacigaba da zuwa shisaiya rinka zama wajanta.nace dashi zandinga zuwa umma domin ganin mutane da yawama zai debemai kewa sosai.tai murna tare dasamana albarka sannan mukayi bangarenmu yana rike da hannuna surutu yake kamar redio har lumshe idanunshi yakeyi sabida dadin surutun yakeji qila. Inashiga daki bayan nagama shirya mana abinda zamuci.yaiwata banna jikina yayi sanyi binayai da ido ganin narafka tagumi ina kallonshi tunanina yanda zan iya gyara wajan. Kamar infasa ihu naji amma yana iya saida nagama gogemai jikinshi sannan nafara gyaran wajan gabadaya yabata wajan da miya da farar shinkafar dana dafamana. Yana zaune yana kallona na fara aikin wajan bakinshi be iyayin shiru jinake kamar namakeshi inhuta. Ihu yafasa tareda cakumata.innalillahi kasama idonka yaji ko gabadaya yagama rudani. Dakyar na samu yabude idon sannan najashi naimai wanka jikina yanata rawa tsabar tsoro domin aduk lokacinda najemai wanka sainayi wannan fargabar dalilin ganinshi azahiri gaskiya daga ganinshi bazaiyima mace hakuriba domin yana famada kaya. . Wani lokacin har addua nake karya warke idan naga abin nashi. Ga kayanan kasa yanda nanunamaka kaji inje ingyara falon. Inashiga falo naji ihunshi da gudu nanufi dakin naikaro da kujera nakifa dakin naiwani karon dashi goshina kamar zaitsage sabida zafi. Naisaurin zagemai ziidin wandon ashewai hadawa yayi da abinshi da wandan yazage shikenan kayi shiru kaji. Garin kwashe miyar nazame nafadi wayyo mama nashiga uku yau wahala zata kasheni Allah kaba wannan bawa naka lfy konima nasamu sassauci. Gobe aiki zanidashi ina tunanin karnaje yaitasani magana ammakuma nasan dole natafi dashi tunda yariga yasaba dani Shiri mukai bana wasaba Ammar yayi kyau sosai matukar ba magana yayiba bazaka gane yarintar tashiba harkasa hada ido nayi dashi domin wani kwarjini na musamman dayaimin nashirya cikin kiriyar atamfa nadora ta aiki sama sannan nasa farin mayami narikemai hannu muka nufi bangaren umma. Hawaye kawai tafara tare dasamin albarka domin ita kanta tana mamakin yanda yaronta yasauya yadawo Ammar dinshi saidai tsabar wauta da wasa dakecin ranshi na lalura. Tai addua taredamana fatan alkhairi narika hannunshi mukai harabar gidan wani farin ciki ke cikin zuciyata domin yau zanfita shikanshi cikin farin ciki yake. Cikin manyan motocinshi nadauki daya. Kowa murna yake da ganina gyare gyare nasa akamin sannan nazauna ina hutawa. Bayan naba Ammar kujerar zama dankarya takurani duba mutane cikin nutsuwa. Aiman abinci zanci.dole nabar komai nakoma kanshi nabashi abaki sannan nacigaba da aikina domin nasan matukar nace dakanshi zaici to wata wahalar zaijawomin. Saiwajan uku nasami kaina Dr.Hafiz yashigo mukafara hirar yaushe gamo Ammar nagefe yanata wasanshi.Dr.Hafiz yace amma Dr.kinsan abinda kedamun wannan guy din. Inafa wlh bansan komaiba kawaidai ummanshi tace zatabani lbr to kuma har yanzu bataimin maganarba kasan nikuma bansan takurama wani shiyasa nai shiru amma wlh abin yana matukar bani mamaki kadaiganshi mutun har mutun amma ba tunanin kirki.kasan Allah kusan kullun sainayi kuka sabida bannarshi to yazanyi nikuma qaddarata kenan. Kici gaba da hakuri da addua ammayakamata kiji labarinshi domin kisan ta yanda zaki temaka mishi. Hakane nagode Dr.Allah yabar zumunci agaidamin da madam nakusayin fishi tunda har yanzu batazo mungaisaba. Bari mu wuce. Oga tashi mutaiko kinabarka nan. Murmushi yayi tareda cewa kukazantayi wlh. Cikin wata biyu naikyau sosai jikina yakara canzawa.ammafa nadan fada. Yayinda Ammar yai kiba yakara wani kyau na musamman hankalinshi kwance yake bashida wata damuwa kullun dashi nake zuwa aiki dana dawo munyi abinda zamuyi saimu wuce wajan umma hira saidare muke komawa. Kannen Ammar nasona sosai domin suna kuladani yanda yakamata abangaren ummama bamagana domin tana gwadamin kauna daidai misali. Yau juma a nida Ammar muka nufi bangaren umma taimana tarba ta musamman kamar yadda tasaba muka gaisa da halimatu da sadiya kannen Ammar sannan nanemi waje nazauna akan kafet mikar da kafafuna yayi sannan ya dora kanshi yai kwanciyarshi yana wasa da yatsun hannuna. Aiman yauzanbaki lbrin mijinki damu kammu insha Allah inafatan ba damuwa.kai umma wane irin damuwa inajinki. Alhaji abdullahi mai yadi hamshakin me kudine masani kan harkar kasuwanci Allah yaimishi hannun kyauta da kaunar talakawa. . Matarshi daya hajiya bilkisu tsawon lokaci basu samu haihuwaba auransu tunna saurayi da bidurwa amma shiru. Hakan yasa alhaji yafara neman aure bayan yagayama matarshi hajiya bilki kuma ta amince domin tasan laifin daga wajanta take. Alhaji yafara neman aurena munhadu da alhaji a makarantar danayi ta scondry domin lokacin yana zuwa wajan abokinshi dayake shine shugaban makarantar anan yaganni yanemi shawarar abokinnashi sannan sukagabatar da kansu wajan yayan nahaifina da mamata ganinsu manyan mutane yasa aka amincemusu sukafara zuwa wajena. Bayan sati biyu da gama makarantana aka dauramin aure da alhaji. Bansami matsala da hajiya bilkiba wajan zamantakewarmu har saida nahaifi Ammar lokacinne alhaji ya maida hankalinshi gabadaya kanshi. Tun lokacinda na lura da hakan na tilastama alhaji daina kulada ammar gaban kowa ammasaiyai biris dani kawayen hajiya sukaita zuguta harta fara bin bokaye. Nafara yin barin duk wani ciki danake dauka bayanna ammar dana haife lfy. Saida nayi bari shidda sannan Allah yabani cikin yan biyu babu wanda yasan inadashi domin inajin alamunshi na matsama alhaji ya maidani gida domin abin yafara bani tsoro lokacinda nakusa haihuwa lokacin hajiya bilki tatafi ganin likita jamany. Agidanmu nahaifi yan biyu alhaji yahada mana shatara ta arziki saida nai arba'in sannan muka koma lokacin ammar yanada shekara 11 haka nacigaba da kula da yarana cikin tausayi da kauna. Daga wannan lokaci bankuma samun cikiba alhaji yamatsa mukaje asbt wani abin mamaki shene gaba daya babu mahaifar ajikina andauketa.babu irin binciken da likitoci basuyiba. Haka muka dawo har alhaji yafini shiga tashin hankali nikuwa tuni naima Allah godiya dayasa masifar tatsaya nan. Ciwon ciki yakama alhaji cikin dare kamin asuba ya rasu.lokacin ammar nada shekara 22 yan biyu nada 11 mutuwarnan ta girgizamu sosai haka muka rungumi qaddara naci gaba da kula da yarana har muka gama takaba.har lokacin ana aikin hada dukiyar alhaji. Sabida rabon gado lokaci haka akazo aka raba wannan gado gaba daya na ammar yafi nakowa wannan bakin cikin wannan yasa hankalin hajiya kin kwanciya. Ko sati biyu ba aiba ammar yafara shaye shaye da neman mata abin ba arziki yakoma bejin kunyata bare tsorona.saidai nakan hana idona barci wajan gayama ubangijina. Haka yaita facaka da kudi danayi magana yace naki ko nawa harna daina kulashi domin naga kamar yanaso yafara zagina abin yana bani mamaki sosai domin nasan ada ammar baya hulda da tantiran yara balle haryakaishi lalacewa haka. Yajima cikin wannan masifa kwatsam kumasai wannan lalurar tasameshi ahakan so hudu munamai aure domin babu wani makusancinshi dazai jurema lalurarshi sai matarshi.amma akayi rashin sa a kowacce bata wata biyu data dibi abinda ta diba saitai waje. Maganar magani kuwa babu kasar daban kaishiba ammadai duk maganar dayace shine kwakwalwarshi qalau take haka komi najikinshi saidai ajira lokacinda zaidawo daidai. Maganar duniya bata buya domin kuwa agari naji anata rade raden hajiyace taimai haka nikuma nasaka sarautar Allah ido domin nasan da amincewar ubangiji tasami nasara kuma nima inafatan yabashi lfy. Nasan cewa bakison ammar kuma suma wa inda suka hada auran sunyine domin su wulakantaki nasan komai aiman amma aishi Allah ba azzalimin bawanshi bane saidaishi bawan yazalinci kanshi.nasan kina zaune da Ammar dan biyayyar iyayenki to nagode sosai kuma insha Allah saikinyi farin ciki da hakan. Idanuna cike da kwalla nace nagode umma Allah yabashi lfy . Kasa hakuri nayi wajan 11 nadare nakira wayar Dr.hafiz domin shine abokin shawarata tunda nasan mama natare da mijinta yanzu. Cikin magagin barci yace Dr.ya akaine zaki tasheni yanzufa nakwanta ko nauyi beyiba. Kaga ni dallah karka tashi matarka koma falo muyi magana nakasa barcin wlh. . Inajinki ya akaine amarya.mitsw kaidai kabani wlh Nan na warwaremai komai hankalinshi yatashi yace lallai biri yayi kama da mutun wlh saidanai tunanin haka domin sihiri gaskiyane kuma yana tasiri akan wanda Allah yaso. To yanzu meyaka muyi Dr.karki damu kibari saimun hade Monday sai musan abinyi ko. Yauwa hafizu nagode sosai Allah yabar zumunci dagaske goben zaka kawamin madam din mugaisa. Insha Allah zaki gammu amma ba zama zamuyiba gidansu zankaita ta dubo abbanta yayi zazzabi. OK bye. Lallabawa nayi na kwanta gefenshi.ya rungumoni hadda sauke ajiyar zuciya tausayinshi yakara kamani. Watana biyu nagabatarma UMMA bukatata tasan zuwa gaida iyayena ba musu ta amsamin ammafa tai jimamin yanda zanbar mata Ammar gida domin yaiwani irin sabo dani kuma nikadai ke hanashi ya hanu. To kuma gaskiya bazanje dashiba yaitamin shirme anamin dariya. Ran asabar na shirya tsaf na lallaba nabarshi wajan umma aboye naimata sallama na silale sai gidan mahaifina domin na tabbata zansameshi gida yanzu. Cikin tsananin farin ciki yatareni oyoyo diyata jikinshi na isa ya rungumeni.ina nane jikinshi muka gaisa yanata murnar ganina wayyo dadyna nikaina nasan yana matukar kaunata kawaidai anashiga tsanina dashine sabida zalunci. Dady aunty batanan ko eh wlh itada hajiya sukafita yanzu hkama yunwa nakeji tunsafe sukafita har yanzu banyi break ba. Dasauri namike wayyo dady sannu ina zuwa cikin kankanin lokaci nashiryamai abinci sannan nagyara jikina nakoma wajanshi yanata samin albarka yabani tausayi sosai koda yake mahaifiyarshi tajamishi saidai hakuri kawai. . Sai wajan azhar nabar gidan nanufi gidan da mamata take aure. Kannena damuke uwa daya su hudu aliyu Umar usman sai ummi suka rungumeni sunata murna nima farin cikin ganinsu domin inasansu sosai. Nabasu tsaraba sannan nasamu suka barni da mama. Saida najini rungume jikinta sannan nasami nutsuwa muka gaisa tanata tambayata yanayin zaman banboyemata komaiba. Alhamdulillah ashema ba mahaukaci bane mutane keta zuzutawa Allah ya kyauta yabashi lfy. Uhumm naci dariya danaga mama ta hadomin magungunan mata.kasa hakuri nayi nace mama yaushe wani abu zaishiga tsakaninmu akwai yarintafa sosai atare dashi ko tsarki nina koyamishi. Dakuwa taimin kinci gidanku to haka zaizauna aidai zaisami lfy ko. Bayan sallar la asar naduba wayata kiran umma yakai shabiyar tsoro yakamani da sauri nakirata. Aiman Dan Allah kidawo hakanan wlh duk yaimana ta adi yanamu kwanciyar hankali banna kawai yake yana kuka. To umma ganinan wlh banji kiran bane. Tuni namike naima mama bayani da uwargidanta da yake tazo dakin mamane munata hira zamansu lfy kansu ahade yake naimusu sallama. Koda nashiga gidan saida na tsorata duk wani abu na glass saidaya fasashi ashe hakayake wannan barna. Kuma har lokacin kuka yake iyakar karfinshi jijiyar kanshi dukta tashi. Ko kallon inda nake beyiba
Thank's for reading my article Ameena Part 1
Created at 2018-12-09 08:10:52

0 Rate upStar
This post has no comments - be the first one! Ameena Part 1
Call Me || Sms Me